Za a ɗauki lokaci mai tsawo duniyar damben zamani ba ta manta da gwarazan da suka fafata a fagen kamar Tyson Fury da Anthony Joshua ba, musamman ta la’akari da yadda sunayen su suka zamo tamkar wani suna ne na wasan damben.
Amma a yanzu za a ci gaba da hasashe ne a kan gwabzawar da ake matuƙar jira ta faru tsakanin gwarazan, kuma tuni fitaccen mai yayata wasan dambe, Eddie Hearn ya yi hasashen cewa karawar za ta zamo mafi ƙayatarwa a tarihin wannan wasa wanda yanzu dai hasashe kawai ake yi game da wanda zai yi nasara tsakanin su.
A watan Disamba Joshua ya doke Otta Wallin, ɗan ƙasar Sweden ɗin da ya zamo wa Fury ƙarfen ƙafa a tsawon shekara huɗu. Ya doke shi ne a zagaye na shida.
Wallin ya shaida cewa ya daɗe yana ganin cewa Fury zai doke Joshua a duk lokacin da suka kara, amma yanzu da ya ɗandana yadda Joshua yake yana ganin karawar tasu sai dai yadda hali ya yi.
Joshua zai sake komawa Saudiyya domin karawa da Francis Ngannou a birnin Riyadh, a ranar juma’a, shi kuma Fury yana gefe yana jiran yadda fafatawar za ta kasance yayin da yake shirya haɗuwar sa da Joshua nan gaba.
Karawar Joshua da Ngannou dai wani zakaran gwajin dafi ne kan abin da zai faru tsakanin sa da Fury, kuma idan ya iya yin nasarar ba-zata akwai alamar zai ƙara tabbata gwarzo a wasan damben Birtaniya.