Home Labaru An Dakatar Da Wasu Sarakuna Gargajiya Biyu A Jihar Zamfara

An Dakatar Da Wasu Sarakuna Gargajiya Biyu A Jihar Zamfara

842
0
An Dakatar Da Wasu Sarakuna Gargajiya Biyu A Jihar Zamfara
An Dakatar Da Wasu Sarakuna Gargajiya Biyu A Jihar Zamfara

Rahotanni sun nuna cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da wasu sarakunan gargajiya biyu.

Sanarwar dai ta fito ne daga ma’aikatar harkokin kananan hukumomi da masarautun jihar, tuni dakatarwar ta fara aiki tun daga ranar Litinin, 27 ga watan Janairu.

Dakatarwar ta shafi sarkin yakin zurmi daga masarautar Zurmi Alhaji Bello Garba Kanwa, da babba uban kasar kanwa Alhaji Muhammad Bello Yusuf na III, da Marafan Bakura.

Mai ba gwamna shawara a kan masarautu Yusuf Abubakar Zulum, ya ce sun samu umurnin ne daga sakataren gwamnatin jihar cewa a dakatar sarakunan bisa wasu laifuffuka da su ka aikata.

Sai dai wasu na zargin dakatarwar ta na da nasaba da belin wasu ‘yan jam’iyyar APC da su ka karba, bayan an kama su tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Leave a Reply