Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ‘yan Nijeriya
su yi hakuri yayin da ya ke kaddamar da wasu sauye-sauye
domin kawo sauyi a kasar nan.
Tinubu ya bayyana haka ne, lokacin da ya kai ziyarar nuna godiya ga Alake na Egbaland Adedotun Gbadebo a fadarsa da ke birnin Abeokuta a jihar Ogun.
Daga cikin tawagar sa akwai mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Malam Nuhu Ribadu, da Shugaban ma’aikatan adar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, da kuma mai magana da yawun shugaban kasa Dele Alake.
Da ya ke jawabi a fadar Alake da ke Abeokuta, shugaba Tinubu ya gode wa shugabannin jam’iyyar APC bisa nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben shugaban kasa, sannan ya yi alkawarin cewa nan ba da dadewa ba ‘yan Nijeriya za su fara samun kyawawan sauye-sauyen da za su yi alfahari da su.














































