Home Labaru Kiwon Lafiya DA DUMI DUMI: Masu Coronavirus Sun Ƙaru Zuwa 184 A...

DA DUMI DUMI: Masu Coronavirus Sun Ƙaru Zuwa 184 A Najeriya

1113
0

Yawan masu cutar Coronavirus a Najeriya ya karu zuwa mutum 184 bayan an samu karin mutum 10 da suka kamu da cutar.

Hakan na zuwa ne yayin da yawan wadanda aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga asibiti ya karu zuwa mutum 20.

A yammacin Alhamis din ne aka sallami mutu 11 bayan sun warke daga cutar a jihar Legas.

Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka, (NCDC) ta fitar da alkaluman, cikinsu cutar har da mutum 2 da suka rasu.

NCDC ta kara da cewa har yanzu jihar Legas ce inda cutar coronavirus ta fi kamari da yawan mutum 98.

Kawo yanzu sauran jihohin da aka samu bullar cutar coronavirus su ne:
Legas – 98
Abuja – 38
Osun – 14
Oyo – 8
Akwa Ibom – 5
Ogun – 4
Edo – 4
Kaduna – 4
Bauchi – 3
Enugu – 2
Ekiti – 2
Rivers -1
Benue – 1