Home Labaru Zargin Rashawa: Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Karbi Rahoton Kwamitin Binciken Abba...

Zargin Rashawa: Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Ya Karbi Rahoton Kwamitin Binciken Abba Kyari

45
0
Abba-Kyari-and-Hushpuppi

Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Alkali Baba, ya karbi rahoton kwamitin da aka kafa don binciken zargin da ake yi wa Abba Kyari kan karbar cin hanci a hannun Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi.

Shugaban kwamitin binciken DIG Joseph Egbunike ne ya mika rahoton ga Akali Baba a ranar Alhamis kamar yadda wata sanarwa da kakakin hedkwatar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba ya fitar.

Sanarwar ta ce rahoton ya kunshi duk bincike kan lamarin, hujjoji, da kuma bahasin da DCP Abba Kyari ya bayar da na sauran mutanen da lamarin ya shafa.

Shugaban ‘yan sandan Najeriya Alkali Baba, ya yabawa kwamitin da wannan aiki da ya yi, yana mai cewa dalilin kafa kwamitin shi ne, a gudanar da sahihin bincike wanda zai taimakawa rundunar ‘yan sanda daukan matakin da ya dace.