Home Labaru Kiwon Lafiya COVID-19: Za A Rufe Tashoshin Jiragen Ƙasa A Nijeriya

COVID-19: Za A Rufe Tashoshin Jiragen Ƙasa A Nijeriya

274
0

Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya NRC za ta rufe jigilar fasinjoji daga dukkan tashoshinta a fadin kasar.

Mataimakin Kakakin hukumar Yakubu Mahmood, ya ce dakatar da sufurin jiragen kasan wani mataki ne na dakile yaduwar cutar coronavirus a kasar.

Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya ya ce, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris da muke ciki.

Jami’in ya kuma ba da hakuri ga masu amfani da jiragen kasa, bisa matsin da matakin zai iya kawowa.

Zuwa yanzu cutar coronavirus ta ke kara yaduwa a kasashen duniya ta kama mutum 22 a Najeriya.

Alamomin bakuwar cutar sun hada da zazzabi da mura mai zafi da tari da kuma sarkewar numfashi.

Hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar su ne da: wanke hannu aikai-akai da kula da tsafta.

A guji amfani da hannu ana taba fuska ko baki ko hanci ko ido.

Akwai kuma nisantar shiga taron jama’a.

A sanya gwiwar hannu a tare baki da hanci idan za a yi tari ko atishawa.

A tuntubi likita idan an ji alamun cutar.

Bin shawarwarin masana da hukumomin lafiya kan matakan kariya daga cutar.