Home Labaru Kasuwanci Coronavirus: ‘Yan Afrika Miliyan 20 Za Su Rasa Aikin Su

Coronavirus: ‘Yan Afrika Miliyan 20 Za Su Rasa Aikin Su

544
0
Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka Ta Dauka
Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka Ta Dauka

Kungiyar Kasashen Afrika ta AU ta ce, annobar coronavirus na iya raba mutane a kalla miliyan 20 da gurabe ayyukansu a fadin nahiyar, abin da ake ganin zai yi wa tattalin arzikin Afrika illa.

Kawo yanzu kashi kalilan Afrika ke da shi daga cikin sama da mutane miliyan 1 da suka kamu da cutar coronavirus a duniya, sai dai tuni tasirin annobar ya durkusar da tattalin arzikin kasashen nahiyar musamman ta fuskokin faduwar farashin gangar danyen man fetur da kuma kauracewar miliyoyin masu yawon bude idon dake ziyartar kasashen.

Kafin barkewar annobar COVID-19, Bankin Raya Kasashen Africa AFDB ya yi hasashen bunkasar tattalin arzikin nahiyar da a kalla kashi 3.4 a wannan shekara, sai dai binciken kungiyar AU ya ce, tasirin annobar murar zai haddasa wa Afrika hasarar kashi 20 zuwa 30 cikin 100 na kudaden da suke samu, kimanin naira biliyan 500 kenan a takaice.

A fannin kasuwanci kadai kuwa, binciken masana tattalin arzikin na Afrika ya yi hasashen kasashen nahiyar za su tafka asarar kimanin Dala biliyan 270 a fannin kasuwanci tsakanin su da kasashen ketare, yayin da kuma a cikin gida gwamnatocin kasashen na Afrika za su kashe karin Dala biliyan 130 kan tattalin arzikin da inganta rayuwar jama’a da fannin lafiya duk a dalilin annobar ta coronavirus.