Home Labaru Kiwon Lafiya Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka

Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka

612
0
Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka Ta Dauka
Coronavirus: Matakan Da Najeriya Ta Dauka Ta Dauka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita na tsawon kwana 14 a jihohin Legas da Ogun da Babban Birnin Tarayya Abuja saboda cutar coronavirus.

Shugaban ya kuma bayar da umurnin mayar da dukkanin filayen wasa da sansanonin alhazai na gwamnatin tarayya zuwa asibitocin da cibiyoyin kula da masu coronavirus.

Ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga ‘yan Najeriya game da annobar cutar coronavirus.

A cikin jawabinsa, Buhari ya shugaban ya kuma nuna kaduwa kan cutar da ke lakume dubban rayuka a kasashen duniya, tare da barazana ga lafiya da tattalin arziki.

Shugaban ya yaba wa jami’an lafiya da dukkan wadanda ke aikin ko suka ba da tallafi ta kowace hanya wurin yakar cutar.

Buhari ya kuma sanar da karin matakan da gwamnatinsa ke dauka domin yakar cutar, da rage radadin tasirinta ga ‘yan kasa. Matakan sun hada da raba kayan tallafi a jihohin da ya sanya dokar hana fita da kuma ba wa ‘ya gudun hijira kayan abinci na wata biyu a cikin makonnin masu zuwa.

Akwai kuma horar da ma’aikatan lafiya; hada wa matalauta kudin tallafin wata biyu a biya su nan take; ciyar da dalibai; da karin wata uku a kan wa’adin biyan rancen da ‘yan kasa suka karba a hannun gwamnati.

Sannan, ya yi da kira ga ‘yan kasar da su ba wa gwamanti baya, sannan mawadata su taimaka wa masu karamin karfi.

Jawabin shugaban kasar na zuwa ne kwanaki bayan wasu ‘yan kasar sun yi ta sukar abin da suka kwatanta da rashin jin duriyar duriyar shugaban kasar kamar sauran kasashen da aka samu bullar cutar COVID-19.

Duk da cewa fadar shugaban kasa da hukumomin kula da cutar kan fitar da sanarwa akai-akai game da halin da ke ciki dangane da cutar coronavirus a kasar, wasu masu shafin zumunta na ganin abin da ya fi dacewa shi ne shugaba Buhari ya fito ya yi musu jawabin karfafa da kansa.

Duk da cewa shugaban kan fitar da sanarwar ta shafinsa na sada zumunta, kuma a baya ma ya yi wata ‘yan gajeruwar bayani game da coronavirus din, masu sukar nasa na ganin hakan bai wadatarba.

‘Yan kasar sun yi ta yayata gangamin neman shugaba Buhari ya fito ya yi musu bayani da taken #WhereIsBuhari.

Wasunsu na bayyana fargabar yadda shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da hadimansa uku suka kamu da cutar, barazana ce ga Buhari, duk da cewa fadar gwamanti da sanar da cewa an yi wa Buhari gwajin cutar kuma ba ya dauke da ita.