Home Labaru Kiwon Lafiya Sai Najeriya Ta Tashi Tsaaye A Kan Coronavirus — Kwararru

Sai Najeriya Ta Tashi Tsaaye A Kan Coronavirus — Kwararru

349
0
Sai Najeriya Ta Tashi Tsaaye A Kan Coronavirus — Kwararru
Sai Najeriya Ta Tashi Tsaaye A Kan Coronavirus — Kwararru

…sun ce akwai barazanar yaduwar coronaviru.

…a mayar da asibitocin koyarwa da na kwararu cibiyoyin gwajin cutar.

Kwararru a fannin lafiya sun ce dole sai gwamnatin Najeriya ta yi tsayin daka wurin shawo kan annobar coronavirus.

Masanan na fargabar cewa muddin Gwamnatin Tarayya ba ta inganta dakunan gwaje-gwajen  cututtukan da ke asibitocinta ta koyarwa 70 ba, akwai yiwuwar yawan masu cutar ya yi tashin gwauron zabi.

Bayan asibitocin koyarwa 70, Gwamnatin Tarayya na da manyan asibitocin 22, baya ga Asibitocin Kwararru da na gama gari fiye da 20,000 a fadin Najeriya, a cewarsu.

A hasashen da suka yi cewa matukar ba a bunkasa asibitocin su rika gwajin cutar coronavirus ba, to cutar na iya yaduwa zuwa kanan yankuna da kauyuka.

Yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke cewa gaggauta yin gwaji shi ne hanya tilo ta shawo kan annobar, kwararru a fannin sun ce gwajin COVID-19 wata babbar dama ce ga Najeriya.

Sai dai duk da yadda cutar ke kara yaduwa a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ba ta jaraba wasu hanyoyin gwajin cutar a jihohin kasar 36 da Babban Birnin Kasar, Abuja ba.

Kawo yanzu dakunan gwaje-gwaje shida ne kacal a fadin kasar ke iya gwajin cutar coronavirus.

Daga cikin dakunan 2 na jihar Legas, 1 a Abuja, 1 a Edo, 1 a Ogun, 1 a Osun.

A fadin jihohin Arewacin kasar 19 kuma babu dakin gwajin cutar ko guda daya.

Jihohi 32 ne a fadin kasar ba su da wurin gwajin cutar coronavirus

NCDC ta ce zuwa ranar 26 ga Maris 2020, ta yi wa mutum 846 gwajin cutar coronavirus a fadin Najeriya.

Shugaban NCDC Dr. Chike Ihekwazu ya ce cibiyar na kokarin kara yawan wuraren wajin COVID-19 a Najeriya zuwa 13.

“Aiki ya yi nisa a Abakaliki, Maiduguri, Kano, Kaduna, Sokoto, Jos, da Fatakwal.

Wani kwararre a Kimiyyar Gwaje-gwajen Lafiya, Dr. Ifeamyi Casmir, ya ce babu kasar da za ta iya shawo kan annoba ba tare da isassun dakunan gwaje-gwaje ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito shi a wata hira ta musamman da ya yi da ita.

Da yake bayyana matakan da Najeriya ke dauka a kan COVID-19 a matsayin fargar jaji, Dr. Casmir ya ce idan har gwamnati ta kasa daukar matakan da suka dace, to da wuya kasar ta iya shawo kan annobar.

Vanguard ta ambato masanin na cewa, “Da irin gwajin da ake yi yanzu, kullum sai karuwa masu cutar suke yi.

“Za a iya samun ci gaba idan aka kara yawan cibiyoyin gwajin cutar.

“Hakan za ta yiwu, duba da irin tallafin da aka samu daga kamfanoni da daidaikun mutane.

“Dole sai mun inganta hanyoyin gwajinmu domin gano masu cutar, mu ware su, a yi musu magani domin magance cutar.

“Duk kasashen da suka yi nasarar rage yaduwar annobar, sun yi amfani ne da cibiyoyin gwawi domin rage yaduwar cutar.”

Shi ma Farfesa Abel Ononu, shugaban Kungiyar Kwararrun Likito ta Najeriya kuma Mataimakin Shugaban kungiyar a Yammacin Afirka, ya ce sakaci ne ya jawo bullar COVID-19 a Najeriya.

Ya ce da tun farko Najeriya ta tsaurara matakan gwaji da killace masu shigowa daga ketare, da tuni ta dakile shigowar cutar cikin kasarta.

Da yake jaddada muhimmancin tsuurara gwajin cutar, Farfesa Ononu ya shaida wa Vanguard cewa:  “Hakan ya hada da kara yawan cibiyoyin gwajin, kuma za a iya amfani da wasu kayan gwajin cutar HIV da ake da su a asibitoci da dama domin gwajin cutar ta coronavirus.”