Home Labaru Cikin Kwanaki Bakwai Da Suka Rage Za A Kawo Ƙarshen Wahalar Sabbin Takardun...

Cikin Kwanaki Bakwai Da Suka Rage Za A Kawo Ƙarshen Wahalar Sabbin Takardun Naira – Buhari

142
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce a cikin kwanaki bakwai da su ka rage da ƙarin wa’adin sauya tsofaffin takardun kuɗi zai maida hankali wajen kawo ƙarshen wahalar da talakawa ke ciki.

Waɗannan, su ne kalaman da shugaba Buhari ya yi wa gwamnonin jam’iyyar APC da su ka ziyarce shi a fadar sa da ke Abuja, inda ya ce zai kira babban bankin kasa da kamfanin buga kuɗi na kasa domin a san yadda za a kawo karshen matsalar a cikin sauran kwanaki bakwai da su ka rage.

Gwamnonin APC dai sun shaida wa shugaba Buhari cewa, lallai su na goyon bayan sauya kuɗin matuka, sai dai wasu sun yi wa abin shigo-shigo ba zurfi su na kokarin rikirkita tsarin, lamarin da ya sa talakawa a jihohin su na fama da tsananin wahala saboda rashin isassun takardun kuɗin.

Haka kuma, gwamnonin sun roki shugaba Buhari ya saka baki, a cigaba da amfani da tsofaffi da sabbin kuɗin har zuwa karshen shekara.

A karshe shugaba Buhari ya ce ya saurari gwamnonin, kuma daga wurin shi zai tabbatar an yi wani abu na gaugawa domin a warware matsalar ƙarancin kuɗin a fadin Nijeriya.

Leave a Reply