A Ranar 29 ga watan Mayu ne ake sa ran Shugaba Bola Tinubu zai jagoranci wani
tattaki na tunawa da shekaru 25 na dimokuradiyyar Najeriya.
Kungiyar masu ruwa da tsaki a harkokin dimokaradiyya ta kasa (NDSG) da ta shirya taron ta bayyana cewa wannan tattakin na daya daga cikin ayyuka da dama da aka tsara domin nuna wannan gagarumin ci gaba.
Kungiyar ta sanar da cewa shugaban kasar ne zai jagoranci tattakin a Abuja tare da rakiyar mataimakinsa, Kashim Shettima. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce, “Makon Dimokuradiyyar Najeriya da aka shirya gudanarwa daga ranakun 10 zuwa 14 ga watan Yuni, 2024, zai zama wani dandali na girmama wannan gagarumin tafiya tare da jaddada sadaukarwarmu tare da gudanar da mulkin dimokradiyya.
“A cikin murnar wannan gagarumin biki, muna mika sakon taya murna ga mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da daukacin ‘yan Najeriya bisa jajircewarsu ga dimokuradiyya da kuma kokarinsu na Ganin sun kare martabarta.














































