Home Home Ci Gaba: Buhari Zai Ƙaddamar Da Aikin Haƙo Mai a Jihohin Bauchi...

Ci Gaba: Buhari Zai Ƙaddamar Da Aikin Haƙo Mai a Jihohin Bauchi Da Gombe

206
0
Fadar shugaban kasa ta shirya kashe Naira Biliyan 14 da miliyan 800 domin sayen Datar hawa shafukan yanar gizo,da  takardu da sauran kudaden da su ka shafi katin waya da na’ura mai kwakwalwa a kasafin shekara ta 2023 da shugaba Buhari ya gabatar.

A ranar Talata ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo mai a Arewa wanda zai gudana a jihohin Bauchi da Gombe.

Aikin wanda zai gudana a yankin Kolmani shi ne irinsa na farko da Arewacin Nijerya ya taɓa gani.

Kimanin shekaru biyu da suka gabata aka gano arzikin man da ke kwance a yankin.

Duk da dai irin wannan aiki ba shi ne farau ba a Kudancin ƙasar, amma wannan shi zai zama karon farko Arewa bayan da matsalar tsaro ta hana aiwatar da makamacin aikin a yankin Borno.

Tun a 2016 Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), ya ƙaddamar da binciken gano mai a wasu jihohin Arewa, inda ya gano arzikin man a jihohi da suka haɗa da Bauchi, Gombe, Borno da kuma Neja.

Leave a Reply