Home Labarai Cbn Zai Rufe Asusun Bankin Da Ba a Haɗa Su Da Bvn...

Cbn Zai Rufe Asusun Bankin Da Ba a Haɗa Su Da Bvn Ba

355
0

Babban Bankin Nijeriya CBN, ya kammala shirin rufe asusun
bankunan da ba a haɗa lambar BVN a jikin su ba, a wani
mataki na ganin an rage zambar yanar gizo a bankuna.

Daraktan sashen kula da tsautsayi na bankin CBN Blaise Ijebor ya bayyana haka a wajen taron buda-baki da aka shirya.

Ijebor, ya ce mazambatan yanar gizo su na amfani da hanyoyi da dama wajen damfarar asusun da ba haɗa shi da BVN ba.

A rahoton da aka fitar a watan Afrilun nan, asusun ajiya miliyan 57 da dabu 100 ne kaɗai da rajistar BVN, daga cikin jimillar asusu miliyan 191 da dubu 400 da aka buɗe a bankunan da ke faɗin ƙasar nan, sannan daga cikin miliyan 191 da dubu 400, miliyan 133 da rabi ne kacal su ke aiki.

Ijebor ya bayyana irin muhimmancin da ke akwai na bankunan da su bi dokoki da sharuɗɗan da suka dace, sannan masu ajiyar su ɗauki matakan kare kai daga zambar yanar gizo.

Leave a Reply