Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dawo sayar da Dala Dala
kai-tsaye ga ’yan canji a kan farashi N1,021.
Sanarwar da bankin ya fitar na sanar da kamfanonin canjin kudade cewa zai rika ba su Dala a kan farashin N1,021. Karo na biyu ke nan a wannan watan na Afrilu da CBN ya rage farashin Dala — bayan na farkon da ya sanya a kan N1,036.
Daga nan babban bankin ya bukaci yan canjin da ke bukata da su tura kudadensu zuwa susun da ya bayar sannan su kai takardun shaidar biya da sauran takardun da ake bukata rassansa domin su karbi Dala.
A cewarsa, hakan na daga cikin matakan farfado da darajar Naira, ganin yadda a yan kwanakin nan ta dan yi kasa.