A jawabin sa na karshe ga ’yan Najeriya a safiyar Lahadi,
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci al’umma su
yafe masa wahalar da canjin kudi ta je fa su a kwanakin baya.
Shugaban kasan ya ce ya kirkiro manufar ce da zuciya daya, domin ya habaka tattalin arzikin Najeriya.
Ya kuma bukaci jama’a su kara yin takatsantsan sannan su ci gaba da ba jami’an tsaro hadin kai domin a kawo karshen matsalar tsaro.
Shugaba Buhari mai barin gado ya ce, a yunkurin sa na bunkasa tattalin arzikin kasa, ya fito da wasu manufofi masu matukar wahala, wadanda galibin su kwalliya ta biya kudin sabulu. Ya ce wasu daga cikin su sun jefa mutane cikin wahala ta dan wani lokaci, saboda haka yana neman afuwar ’yan uwa ’yan Najeriya, amma da zuciya daya ya kirkire su.