Home Labaru Rashin Takardu: Maniyatan Filato 100 Sun Makale A Tashar Jirgin Saman Bauchi

Rashin Takardu: Maniyatan Filato 100 Sun Makale A Tashar Jirgin Saman Bauchi

55
0

Yanzu haka maniyata aikin Hajin bana 100 ne daga Jihar Filato
suka makale a filin jirgin saman Bauchi saboda gazawar
gwamnatin jihar na biya musu kudaden kujerar alfarmar da aka
basu.


Yayin da aka fara jigilar maniyata aikin hajjin bana zuwa kasar Saudi Arabia, wadannan maniyata sun shiga cikin rudu da dimaucewa saboda yadda ta tabbata cewar ba za su cimma burin su na sauke farali ba, sakamakon rashin fitowar sunayen su a cikin jerin sunayen masu tafiya da aka biya musu kudade


Da ya ke tabbatar da hakan a filin Jiragen Sama na Bauchi, Darektan sashin gudanarwa a Hukumar Alhazai ta Jihar Plateau, Alhaji Isa Hashimu Salihu, ya ce wadanda matsalar ta shafa su ne maniyatan da suka samu kujerun alfarma na gwamnati. Ya ce gwamnatin jihar ta tura kudaden kujerun alfarma guda
100 da ta saya don raba wa jama’ar ta amma a makare, lamarin da ya shafi tafiyar maniyatan.


Sai dai wasu bayanai na daban na nuna cewar gwamnati mai barín gado bata mikawa hukumar alhazai ta tarayya kudaden wadannan maniyata 100 bane, dalilin da ya sa suka makale a tashar jiragen. Maniyatan da abin ya shafa, sun bayyana takaicinsu kan wannan al’amari da suka kira a matsayin yaudara da gangan, musamman

Leave a Reply