Home Labaru Kasuwanci Bunkasa Kasuwanci: CBN Na Kokarin Fara Amfani Da Kudin Intanet Na E-Naira

Bunkasa Kasuwanci: CBN Na Kokarin Fara Amfani Da Kudin Intanet Na E-Naira

204
0

Babban bankin Najeriya wato CBN ya sanar da sunan kamfanin fasahar da zai yi aiki da shi, a kokarin fara amfani da kudin intanet na e-Naira.

CBN ya zabi kamfanin Bitt  daga cikin manyan kamfanonin fasaha da dama da suka fafata wajen ganin sun samu kwangilar aiki tare da Bankin domin samar da wannan kudi cikin tsaro da tsari mai inganci.

A cewar Bankin ya fi gamsuwa da kamfanin Bitt. saboda wasu tsare-tsare da gwaje-gwaje da ya aiwatar kan kudin intanet, wanda dama tuni kudin da kamfanin ya samar an soma kashe su a kasashen gabashin Caribbean.

Sanarwar da CBN ya fitar ta kuma shaida cewa CBN ta lissafa wasu daga cikin alfannu kudin intanet din da suka hada da inganta tsarin kasuwanci tsakanin iyakoki, wadatuwar kudade cikin sauki da kuma saukin kasafi da haraji.

Leave a Reply