Home Labaru Bukukuwa: Gwamnati Ta Bada Hutun Bikin Kirsimeti Da Na Sabuwar Shekara

Bukukuwa: Gwamnati Ta Bada Hutun Bikin Kirsimeti Da Na Sabuwar Shekara

263
0

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Juma’a 25 da Litinin 28 ga watan Disamba na shekara ta 2020, da kuma ranar Juma’a 1 ga watan Janairu a matsayin ranakun hutun bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da babban sakataren ma’aikatar Dakta Shu’aibu Belgore ya fitar.

Yayin da ya ke taya kiristoci murnar bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara, Aregbesola ya bukaci kiristoci su yi koyi da koyarwar Annabi Isah da su ka hada da imani da kuma kauna.

Ya ce ya zama dole su yi koyi da rayuwar saukin kai, hidima da tausayi da hakuri da zaman lafiya da kuma tsoron Allah da Annabi Isah (AS) ya siffantu da su.

Ministan ya kara da cewa, zaman lafiya da tsaro abubuwa ne da ke da muhimmanci, wadanda za su ba gwamnati damar farfado da tattalin arziki da janyo hankulan masu saka hannun jari da samar da ayyuka ga miliyoyin matasa a cikin shekaru 10 masu zuwa.