Sarkin Salman na Saudiyya ya yi kiran a yi sallar rokon ruwa a faɗin ƙasar baki ɗaya a ranar Alhamis, kamar yadda gidan sarautar ƙasar ya fitar a wata sanarwa jiya Talata.
Sarkin ya yi kiran a yi sallar ta Istisqa, ne kamar yadda yake a Sunnar Annabi Muhammad (SAW), idan ana cikin buƙatar ruwan sama.
Haka kuma Sarkin ya buƙaci dukkan Musulmi su yi addu’o’in neman gafara da tuba ga Allah (SWT), kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Sudiyyar ya ruwaito a sanarwar.
Sannan kuma ya yi kira ga jama’a su ƙara abubuwa na alheri da neman kusanci ga Allah (SWT), kamar sadaka da addu’o’i don neman rahama da sauƙin rayuwa da kuma jinƙai daga Ubangiji.