Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai ƙaddamar babbar
matatar Man da hamshaƙin ɗan kasuwa Aliko Dangote ya
gina.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bashir Ahmad, ya ce za a ƙaddamar da katafariyar matatar man da aka fara ginawa tun shekara ta 2016 nan da makonni biyu masu zuwa.
Kamfanin Aliko Dangote dai ya gina matatar ne, wadda za ta iya tace gangar mai dubu 650 a kowace rana, da nufin magance shigo da tataccen mai daga kasashen ketare.
Bashir Ahmad, ya ce Buhari zai ƙaddamar da matatar ne a ranar 22 ga watan Mayu na shekara ta 2023.
Ana dai tunanin matatar ta laƙume kudi kimanin dala biliyan 19, fiye da yadda aka yi hasashen za ta laƙume tun farkon fara gina ta, sakamakon jinkirin shekaru da aka samu wajen gina ta.
You must log in to post a comment.