Home Labaru Hukumar Kula Da Ɗa’Ar Ma’Aikata Ta Buƙaci Tinubu Ya Bayyana Kadarorinsa

Hukumar Kula Da Ɗa’Ar Ma’Aikata Ta Buƙaci Tinubu Ya Bayyana Kadarorinsa

355
0

Hukumar kula da Da’ar Ma’aikata ta Nijeriya, ta ce dole ne
zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin
sa Kashim Shettima da gwamnonin da ke jiran rantsuwa su
bayyana kadarorin su kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Haka kuma, hukumar ta ce zaɓaɓɓun ‘yan majalisun wakilai da na dattawa ma za su bayyana nasu kadarorin kafin ranar 5 ga watan Yuni, lokacin da za a rantsar da su.

Rahotanni sun ambato mai magana da yawun hukumar Mrs Veronica Kato ta na cewa, bayyana kadarorin wani ɓangare ne na shirye-shiryen shan ratsuwar kama aiki ga zaɓaɓɓun shugabannin kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.

Ta ce da yawa daga cikin zaɓaɓɓun shugabannin sun fara karɓar fom na bayyana kadarorin a rassan ofisoshin hukumar da ke faɗin Nijeriya, kuma ana sa ran za su maida shi zuwa ofisoshin tare da bayyana kadarorin kafin ranar da za a rantsar da su.

Kundin tsarin mulkin Nijeriya dai ya yi tanadin cewa, masu riƙe da muƙaman siyasa su bayyana kadarorin da su ka mallaka a lokacin da za su kama aiki da kuma a lokacin da su ka kammala wa’adin mulkin su.

Leave a Reply