Home Labaru Buhari Ya Naɗa Kwamitin Mutum 14 Kan Ƙarancin Man Fetur A Nijeriya

Buhari Ya Naɗa Kwamitin Mutum 14 Kan Ƙarancin Man Fetur A Nijeriya

114
0

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya amince da wani kwamitin mutane 14 domin samar da albarkatu da kuma bibiyar ƙa’idojin farashin man fetur.

Wannan dai ya na zuwa ne, a daidai lokacin da masu amfani da albarkatun man fetur ke nuna ɓacin ran su, game da taɓarɓarewar ƙarancin sa a cikin tashin farashin da ba a ƙayyade ba.

Yayin da wasu ‘yan tsiraru a ɓangaren man fetur su ka yaba da kafa kwamitin, wasu kuma sun ce shugaba Buhari da muƙarraban sa na fafatawa da lokaci.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaba Buhari zai jagoranci kwamitin gudanarwa da kan sa yayin da karamin ministan albarkatun man fetur Timipre Sylva zai kasance mataimaki.

Buhari ya kuma umurci kwamitin ya tabbatar da tsarin kula da hajoji na ƙasa, da hangen nesa a kan shirin gyara matatun mai da kuma tabbatar da bin diddigin albarkatun man fetur, musamman farashi domin tantance yadda ake amfani da shi a kullum da kuma kawar da fasa-ƙwauri.

Leave a Reply