Home Ilimi Buhari Ya Amince a Buɗe Sabbin Polytechnic a Wasu Jihohi Uku Buhari

Buhari Ya Amince a Buɗe Sabbin Polytechnic a Wasu Jihohi Uku Buhari

84
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da bude
Kwalejojin kimiyya da Fasaha na tarayya guda uku, a matsayin
hanyar saukaka wa jama’a damar samun ilimin gaba da
sakandare a Nijeriya.

Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta
tarayya Ben Bem Goong ya bayyana haka a cikin wata sanarwa
da ya fitar a Abuja.

Ya ce makarantun uku sun hada da ta Umunnoechi da ke Jihar
Abia da Orogun a Jihar Delta da kuma Kabo a Jihar Kano.

Mai ba shugaban kasa shawara a kan kafafen sadarwa na zamani
Bashir Ahmad ya tabbatar da rahoton kafa kwalejojin uku a
shafin sa na Twitter, inda ya ce kwalejojin za su fara aiki ne a
watan Oktoba na shekara ta 2022.