Home Labaru Buhari Ya Ƙirƙiri Hukumar Kare Bayanai Da Sirrin Kasa NDPB

Buhari Ya Ƙirƙiri Hukumar Kare Bayanai Da Sirrin Kasa NDPB

46
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da kafa sabuwar hukumar kare bayanai da sirrin kasa a zamance mai suna ‘Nigeria Data Protection Bureau’ NDPB a Turance.

An dai kafa hukumar ne, bayan Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani Farfesa Isa Ali Pantami ya bukaci a kafa ta.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin Pantami, mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Uwa Suleiman, ta ce an kafa hukumar ne bisa tsari mafi kyau, wanda zai mada hankali wajen kare bayanai da sirrin kasa da wasu ayyuka.

Ta ce bayan samun nasarar aiwatar da tsarin zamantar da tattalin arzikin Nijeriya, hukumomi da dama sun zamantar da ayyukan su.

Shugaba Buhari, ya kuma amince da bukatar Pantami ya nada Dr Vincent Olatunji a matsayin shugaban hukumar, kuma nadin zai fara aiki nan take.