Home Labarai Bincike: Babbar Alkalin Jihar Zamfara Ta Kaddamar Da Kwamiti Kan Mataimakin Gwamna...

Bincike: Babbar Alkalin Jihar Zamfara Ta Kaddamar Da Kwamiti Kan Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu

88
0
Babbar alkalin Jihar Zamfara Mai Shari'a Kulu Aliyu, ta rantsar da kwamatin mutum biyar da zai binciki laifukan da ake zargin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau na rashin ɗa'a.

Babbar alkalin Jihar Zamfara Mai Shari’a Kulu Aliyu, ta rantsar da kwamatin mutum biyar da zai binciki laifukan da ake zargin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau na rashin ɗa’a.

Kwamatin ƙarƙashin tsohon Alƙali Tanko Soba, an kafa shi ne sakamakon damar da kundin tsarin mulki ya ba alƙali, a cewar Mai Shari’a Kulu.

Ta ƙara da cewa Sashe na 185(5) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ne ya ba ta damar kafa kwamatin sakamakon buƙatar da Majalisar Dokokin Zamfara ta gabatar mata ranar 10 ga watan Fabarairu ta ƙorafi kan mataimakin gwamnan.

A gefe guda kuma, Babbar Kotun Abuja ta tsaida ranar 10 ga watan Maris don fara sauraron ƙarar da Mahdi Gusau ya shigar yana neman kotun ta dakatar da yunƙurin tsige shi da ‘yan majalisar ke yi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya ɗaga zaman a ranar Talata, yana mai umartar ɓangarorin su kimtsa kafin ranar ci gaba da shari’ar.

A ranar Alhamis da ta gabata ne ‘yan majalisar 18 cikin 22 suka amince a tsige mataimakin gwamnan wanda har yanzu yake a jam’iyyar adawa ta PDP sakamakon zargin sa da laifin rashin ɗa’a.