Home Home Bin Doka: El-Rufa’i Ya Umurci Ma’aikata Su Ajiye Aiki Bisa Saboda Sha’awar...

Bin Doka: El-Rufa’i Ya Umurci Ma’aikata Su Ajiye Aiki Bisa Saboda Sha’awar Mukamin Siyasa

112
0
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa’i, ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da sauran ma’aikatan da ke neman tsayawa takara a shekara ta 2023 su yi murabus daga ranar 31 ga watan Maris na shekara ta 2022.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa’i, ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da sauran ma’aikatan da ke neman tsayawa takara a shekara ta 2023 su yi murabus daga ranar 31 ga watan Maris na shekara ta 2022.

Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Muhammad Sani Abdullahi Dattijo, kuma tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Kaduna ne kadai ya bayyana aniyar tsayawa takarar neman kujerar El-Rufai.

Dattijo, ya ce idan aka zabe shi zai karfafa nasarorin da gwamna El-Rufa’i ya samu wajen ciyar da jihar Kaduna gaba.

A cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna Balarabe Abbas Lawal ya fitar, ya ce dokar zabe ta shekara ta 2022 da Shugaba Buhari ya sanya wa hannu c eke kunshe da wannan ka’ida.

Sanarwar ta ce, dokar ta tanadi cewa irin wadannan jami’an su yi murabus kwanaki 30 kafin zaben fidda gwani na kujerar da su ke nema, don haka duk masu rike da mukaman siyasa da sauran ma’aikatan gwamnati da ke neman mukaman siyasa su mika takardar barin aiki ga sakataren gwamnatin jihar kafin ranar 31 ga watan Maris na shekara ta 2022.