Home Labaru Bilyaminu Ismail Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Zamfara Karo Na 7

Bilyaminu Ismail Ya Zama Shugaban Majalisar Dokokin Zamfara Karo Na 7

314
0

Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara, ta zabi shugaban ta a karo
na bakwai daga mazabar Moriki da ke Karamar Hukumar
Zurmi ta Arewa, yayin da Adamu Aliyu ya kasance
mataimakin sa daga mazabar Gumi ta biyu.

Akawun Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara Shehu Sa’idu Anka ne ya jagoranci zaben shugabanin majalisar.

Rahotanni sun ce, nan take Akawun Majalisar ya rantsar da Shugabanin Majailisar kamar yadda doka ta tanada.

Haka kuma, shugaban Majalisar Honarabul Bilyaminu Ismail ya rantsar da sauran shugabannin kwamitocin majalisar domin fara aiki nan take.

Leave a Reply