Hamshaƙin ɗan kasuwa Aliko Ɗangote da takwaran sa Bill
Gates, sun taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cire
tallafin man fetur da ya yi da sauran nasarorin da ya samu ya
zuwa yanzu.
Ɗangote ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, jim kaɗan bayan ganawar su da Shugaba Tinubu a ofishin sa.
Aliko Dangote, ya ce ana sa ran cire tallafin ya zama mabuɗin hanyoyin samun ƙarin kuɗaɗe ga ƙasa, domin gwamnati ta samu zarafin zuba jari a sauran fannoni irin su ilimi da ababen more rayuwa da sauran su saboda amfanin talakawa.
Ya ce ziyarar ta musamman ce, kuma wata dama ce ta labarta wa Shugaba Tinubu harkokin Gidauniyar Bill Gates da ta Aliko Ɗangote, yayin da su ke fatan Gwamnatin ta ƙara himma wajen inganta fannin kiwon lafiya a Nijeriya.