Home Labaru Bikin Sallah: An Yaba Wa Al’ummar Musulmi A Jihar Kaduna

Bikin Sallah: An Yaba Wa Al’ummar Musulmi A Jihar Kaduna

551
0

An yaba da yunkurin al’ummar musulmi musamman a jihar kaduna na ganin marayu da sauran marasa galihu sun gudanar da bukukuwan sallar su cikin annashuwa da jin dadi.

Shugaban kwamitin raba kayan marayu na kungiyar Izala a yankin karamar hukumar kaduna ta kudu Malam Muhammad Jibril Sabon Naira, ya yi yabon a sakon taya al’ummar musulmin duniya murnar gudanar da bukukuwan sallah.

Sabon Naira, ya ce ya yi farin cikin ganin yadda al’ummar musulmi a jihar kaduna suka bada hadin kai wajen bada gudumuwar su ga shirin na taimakawa marayu, sai ya yi fatar idan Allah ya kaimu badi za’a rubanya fiye da haka.

A wani bangaren kuma kansilan Barnawa Bello Musa Mato, ya mika sakon taya murnar ga daukacin al’ummar musulmin duniya, da Najeriya, da jihar kaduna da kuma gundumar Barnawa kan yadda ake cigaba da gudanar da bukukuwan sallah lami lafiya.

Bello Musa Mato, ya ce a matsayin sa na matashi, yana kira ga matasa su yi murnar sallah cikin natsuwa su guji ganganci da aikata duk wani abu da zai zai iya kawo rashin natsuwa a cikin al’umma.