Home Labaru Bello Turji Ya Sako Mutum 20 Da Yaran Sa Su Ka Yi...

Bello Turji Ya Sako Mutum 20 Da Yaran Sa Su Ka Yi Garkuwa Da Su

116
0

Ƙasurgumin shugaban ‘yan bindiga Bello Turji, ya sako
mutane 20 da aka yi garkuwa da su, wadanda ke tsare a
sansanonin sa daban-daban a yankunan Zamfara ta Arewa da
sassan jihar Sokoto.

Daga cikin waɗanda aka sako akwai wata matar aure da aka ɗauke mako ɗaya bayan auren ta, da kananan yara uku, da tsofaffi uku da wasu da aka ɗauke a gonakin su da kan hanya.

An dai sako mutanen ne bayan an kwashe kwanaki 53 a hannun ‘yan bindigar, inda su ka riƙa kwanciya cikin ruwa da rana sannan yaran ‘yan bindigar su na azabtar da su.

Mutanen sun ce, akwai sama da sansanonin ‘yan bindiga 20 a dajin Manawa, waɗanda su ke cike da ‘yan bindiga masu ɗauke da miyagun makamai, kuma a kullum baƙi su na zuwa domin kai masu bindigogi da alburusai da sauran kayayyaki.

Sun ce sako su da Bello Turji ya yi ya faru ne sakamakon wani sulhu da aka yi, wanda a cewar su an yi ne da wasu jami’an gwamnati da su ke tunanin sun je ne daga Abuja.

Leave a Reply