Home Labaru Bayyana Kadara: Babban Jojin Nijeriya Ya Ce A Ladabtar Da Jojin Abuja

Bayyana Kadara: Babban Jojin Nijeriya Ya Ce A Ladabtar Da Jojin Abuja

157
0

Shugaban Alkalan Nijeriya Tanko Muhammad, ya bada umarnin a ladabtar da Alƙalin Kotun Abuja, saboda ya yi kasassaɓar aika wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Charles Soludo sammaci na aikata laifin da bai aikata ba.
Yanzu haka dai, Soludo shi ne ɗan takarar gwamnan Jihar Anambra a ƙarƙashin jam’iyyar APGA.


Alƙalin mai suna Gambo Garba da ke Babbar Kotun Shari’a da ke Zuba, ya aika wa Soludo sammwcin ne a cikin watan Yuli, bisa zargin bai bayyana yawan kadarorin sa ba a lokacin da ya ke Gwamnan CBN, tsakanin ranar 29 ga watan Mayu na shekara ta 2004 zuwa 29 Mayu na shekara ta 2009.


Wani mai suna Oliver Butrus ne ya shigar da ƙorafi a kotun, cewa a lokacin da Soludo ya ke Gwamnan CBN ya karya dokar hukumar kula da da’ar ma’aikata tunda bai bayyana yawan kadarorin sa ba.
Ya ce har yau babu wanda ya san halastacciyar dukiyar da Soludo ya tara, tunda bai bayyana yawan kadarorin sa ba kamar yadda dokar Nijeriya ta gindiya.

Leave a Reply