Home Labaru Neman Hakki: ‘Yan Majalisun PDP Sun Maka Kakakin Majalisa Kotu A Cross...

Neman Hakki: ‘Yan Majalisun PDP Sun Maka Kakakin Majalisa Kotu A Cross Rivers

175
0
PDP

‘Yan jam’iyyar PDP bakwai daga cikin ‘yan majalisar dokoki ta jihar Cross Rivers da ba su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC ba sun maka kakakin majalisar da wasu mutane 17 kotu.


Wata majiya ta ce, ‘yan majalisar sun shigar da ƙara kotu ne da bukatar a biya su hakkokin su da aka rike.
Haka kuma, ‘yan majalisar sun yi zargin cewa, an rike ma su hakkokin su na tsawon watanni, bayan sun ƙi amincewa su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tare da sauran takwarorin su da su ka mara wa gwamna Ayade baya.


‘Yan majalisar na jam’iyyar PDP, sun shigar da ƙarar ne a kotun da ke kan hanyar Moore a cikin birnin Calabar na jihar Cross Rivers.
Rahotanni sun ce, kotun da ɗage sauraren karar zuwa ranar 14 ga watan Satumba, biyo bayan shigar da bukatar hakan daga ‘yan jam’iyyar APC.

Leave a Reply