Tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, ya shawarci takwarorin sa na jihohin Imo da Ogun, su mika kan su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC.
Fayose, ya bukaci Rochas Okorocha ya yi koyi da shi, sannan ya mika kan sa ga hukumar yaki da rashawar EFCC, yayin da ya shawarci EFCC cewa kada ta daga wa Ibikunle Amosun kafa.
Ayodele Fayose, ya ce ya san irin wannan rana ta na zuwa, kuma kofa a bude ta ke domin Okorocha ya zo ya hadu da shi.
Idan dai za a iya tunawa, wasu rahotanni sun ce Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC sun kama Rochas Okorocha da matar sa Nkechi Okorocha, amma hukumar ta musanta labarin.
You must log in to post a comment.