Home Labaru Eid-Fitri: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranakun Talata Da Laraba A Matsayin Hutu

Eid-Fitri: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranakun Talata Da Laraba A Matsayin Hutu

294
0

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata 4 ga watan Yuni da Laraba 5 ga wata a matsayin ranakun hutun murnar karamar Sallah.


Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da ta samu sanya hannun Daraktan kula da harkokin yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kula da harkokin cikin gida Mohammed Manga a Abuja.


Sanarwar ta taya al’ummomin Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, sannan ta bukacesu da su yi amfani da damar wajen yiwa kasa addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba.


Ta bukaci ‘yan Najeriya da su guji muggan kalamai da ka iya rarraba kawuna da kuma haifar da tashin-tashina a tsakanin al’umma, musamman a wannan lokaci.


Sanarwar ta kuma bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da hada hannu da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a kokarin da take na sake gina Najeriya ta hanyar samar da ababen more rayuwa, da ci gaban kasa.