An cika wata 4 cur da kuskuren harin da sojoji suka kai garin Tudun Biri na Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna, sai dai har yanzu gwamnati ba ta biya diyyar ko da mutum guda cikin dimbin mutanen da harin ya kashe ba.
A ranar 3 ga watan Disamban bara ne dai wani hari da sojojin Najeriya suka kai da jirage marasa matuka ya kashe tarin mutanen da ke tsaka da taron mauludi a garin na Tudun Biri lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar kasa.
Tun a kwanaki kalilan bayan faruwar harin ne gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta sha alwashin biyan diyyar daukacin mutanen da harin sojojin ya kashe da yawan su ya haura 120 baya ga sake gina kauyen baki daya.
Malam Auwal Shehu wanda ya rasa yaron sa guda sai kuma yarinyar sa daya da ta jikkata ya ce har zuwa yanzu bai samu diyyar ba, sai dai zaman jiran tsammani, yayin da Jafar Abdullahi wani mazaunin garin ke cewa iyakar kudaden da al’ummar garin suka samu kawo yanzu shi ne tallafin dubiya da masu ziyara ke ba marasa lafiya a asibiti.














































