Fadar shugaban ta yi karin haske a kan bada tabbacin matsayar shugaba Buhari a kan samar da ‘yan sandan jihohi a fadin Nijeriya.
Fadar shugaban kasa ta ce, batun amincewar shugaba Buhari na bada izinin samar da ‘yan sandan jihohi a kanzon kurege ne.
Ingantattun majiyoyi da dama sun ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta musanta rahotanni da su ka bayyana amincewar shugaban kasa na samar da ‘yan sandan jihohi.
Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu ya bayyana haka a Abuja.
Ya ce bayan karbar sakamakon bincike da kwamitin shugaban kasa ya gudanar a kan samar da ‘yan sandan jihohi a Nijeriya, shugaba Buhari ya bukaci tsawon watanni uku domin zurfafa tunani tare da gudanar da dogon nazari na yiwuwar hakan a Nijeriya.