Home Labaru Takaddama: Majalisar Shari’a Ta Kasa Ta Aminta Da Ritayar Onnoghen – Buhari

Takaddama: Majalisar Shari’a Ta Kasa Ta Aminta Da Ritayar Onnoghen – Buhari

351
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi karin haske a kan lamarin tsohon shugaban alkalan Nijeriya mai shari’a Walter Onnoghen.

Daftarin mai dauke da karar da gwamnatin tarayya ta shigar a madadin shugaba Buhari da ministan shari’a, ya na nuna amincewar majalisar shari’a ta kasa a kan ritayar Onnoghen.

Haka kuma, Daftarin ya yi bayanin cewa, bisa korafin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta shigar, hakan ya zama wajibi ga shugaban alakalan ya yi ritaya saboda ya saba dokar kasa.

Lamarin kuwa, ya zo daidai da kudurin majalisar shari’a ta kasa, wadda ita ma ke goyon bayan shugaban alkalan ya ajiye aiki ta hanyar fito da batun fili tun ranar 5 ga watan Afirilu na shekara ta 2019.

Babban sakataren ma’aikatar shari’a ta tarayya Mista Dayo Apata ya shigar da wannan kara, inda ya ke wakiltar bangaren gwamnatin tarayya a kotun.

Sai dai bangaren wanda ake kara ya nemi a dakatar da tabbatar da mukaddashin shugaban alkalan Nijeriya mai shari’a Tanko Muhammad a matsayin shugaban alkalan na dindindin.