Home Labaru Bashi: Shugaban Barcelona Joan Laporta Ya Ce Ana Bin Kungiyar Fam Biliyan...

Bashi: Shugaban Barcelona Joan Laporta Ya Ce Ana Bin Kungiyar Fam Biliyan 1.15

62
0
Barcelona374

Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya ce ana bin kungiyar bashin fam biliyan 1.15, ya kwatanta lamarin da abin damuwa.

Yace Kudin albashin da kungiyar ke biya ya kai kaso 103 na cikin kudin da take samu.

Laporta ya zargi tsohon shugaba, Josep Maria Bartomeu da cin wadannan bashin kuma ya bar baya da kura.

Shugaban Barcelona, Laporta ya ce wanda ya gada Josep Maria Bartomeu ne ya yi masa karya.

Yace da Barcelona ta tsawaita kwantiragin Messi, kudin albashin zai kai kaso 110 cikin 100 na kudin shiga, wanda mahukuntan La Liga suka ki amincewa.

A makon jiya ne dai Messi ya yi ban kwana da Camp Nou ya kuma sa hannu kan kwantiragin kaka biyu a Paris St Germain, wadda ta gabatar da shi ranar Asabar.