Home Labarai Bashi: Hukumar Birnin Tarayya Ta Rufe Ma’Aikatar Tsaro Da Wasu Ma’Aikatun Gwamnati

Bashi: Hukumar Birnin Tarayya Ta Rufe Ma’Aikatar Tsaro Da Wasu Ma’Aikatun Gwamnati

19
0

Hukumar birnin tarayya Abuja, ta rufe wasu ma’aikatu sakamakon tulin bashin naira biliyan 10 da ta ke bin su.

Ma’aikatu da hukumomin da lamarin ya shafa kuwa sun hada da
da ma’aikatar ayyuka da gidaje da ma’aikatar tsaro da ta lafiya
da Hukumar muhalli da Ma’aikatar kasuwanci da Zuba Jari, da
Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Tsaro ta Civil Defence.

Wata majiya ta ce, tun farko hukumar ta Kai ma’aikatun Kara,
inda kotun ta umurci su bayyana gaban ta a ranar 30 ga watan
Maris, amma su ka ki halarta.

Shugaban hukumar Osilama Braimah, ya ce hukumar ta na bin
ma’aikatar ayyuka da gidaje Naira Miliyan 9 da dubu 998 da
625, yayin ake bin ma’aikatar tsaro naira Miliyan 17 da dubu
220 da 775, hukumar gyaran Hali kuma Naira Miliyan 10 da
dubu 128 da 906 da Kobo 25, sai kuma hukumar tsaro ta civil
defence da ake bi Naira Miliyan 2 da dubu 451 da 649 da Kobo
50, hukumar tara haraji kuma naira miliyan 21 da dubu 683 da
750.00.

Saura sun hada da ma’aikatar lafiya da ake bi Naira miliyan 14
da dubu 204 da 843 da Kobo 75, ma’aikatar kasuwanci da zuba
jari kuma Naira Miliyan 19 da dubu 222da 287 da Kobo 50,
ma’aikatar ilimi kuma Naira Miliyan 25 da 838 da 275.