Home Labarai An Gano Ma’Adannan Karkashin Kasa Fiye Da Talatin A Jihar Nasarawa

An Gano Ma’Adannan Karkashin Kasa Fiye Da Talatin A Jihar Nasarawa

82
0

Gwamnatin Jihar Nasarawa, ta ce ta gano ma’adanan karkashin kasa sama da talatin, wadanda ta ke da yakinin sarrafa su zai janyo ingantar tattalin arziki da kawo saukin masifun rashin tsaro da Nijeriya ke fuskanta.

Ana dai yi wa Jihar Nasarawa kirari da ‘Gidan Ma’adanai’,
saboda irin nau’u’kan ma’adanan da ke dankare a karkashin
kasar ta, bangaren da gwamnatocin baya su ka yi wa rikon
sakainar kashi.

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule, ya ce yanzu
haka sun samo manyan kamfanonin da za su zuba jari a
bangaren ma’adanan domin bunkasa su da farfado da wasu
hanyoyin samar da arziki a Nijeriya.

Yawancin wuraren da ake samun ma’adinai a Nijeriya dai a kan
samu rigingimu, lamarin da gwamnan ya ce su na bin matakan
da su ka dace don hana tashin hankali.

Gwamnatin tarayya dai ta ce ta na sane da albarkatun kasa fiye
da arba’in da hudu, wadanda ake amfani da su a masana’antu da
sarrafa makamashi, kuma za su iya sauya rayuwar mutane sama
da miliyan dari biyu.