Wasu da ake zaton ‘yan bindiga ne, sun ba wata makarantar sakandare da ke garin Jangebe a Karamar hukumar Talatar Mafara ta jihar Zamfara hutun dole har na tsawon makonni biyu.
Wata majiya ta ce an wayi gari kawai aka ga wata takarda manne a kofar ofishin shugaban makarantar, inda aka rubuta cewa daga ranar 1 ga watan Nuwamba kada wani dalibi ko malami ya sake zuwa makarantar har sai bayan kwanaki 14.
Tuni dai lamarin ya sa dalibai da malamai su ka bi umarnin ta hanyar kaurace wa makarantar.
Sai dai wasu na ganin ‘yan bindiga ne su ka manna takardar, domin a ciki sun rubuta cewa, idan ba a bi umarnin ba lallai za su babbake makarantar gaba daya.
Rundunar
Soji da ke aikin samar da tsaro a jihar Zamfara, ta ce ta na nazari a kan
wasikar, sannan za ta bi diddigin lamarin.
You must log in to post a comment.