Home Labaru Babban Hafsan Soja Ya Danne Kudaden Gina Asibitoci Da Makarantu

Babban Hafsan Soja Ya Danne Kudaden Gina Asibitoci Da Makarantu

422
0
Umar Dikko, Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama
Umar Dikko, Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama

Kallo ya koma sama a wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda wani mai gabatar da shaida ya fallasa yadda Tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama Umar Dikko ya yi rub-da-ciki a kan wasu bilyoyin kudade.

Daga cikin bilyoyin kudaden da mai bada shaidar Hammadama Bello ya bada, har da bayani a kan yadda Dikko ya danne naira bilyan 1 da miliyan 200 na kudaden da aka ware domin gina makaranta a barikin sojin sama na Kano, da gina asibiti a Yola da Kaduna da Kado da Abuja da kuma kudaden aikin gyaran barikokin sojojin sama.

Hammadama Bello dai shi ne mai shaida na 9 da hukumar EFCC ta gabatar, inda ya shaida wa kotu cewa Umar Dikko ya karkatar da kudaden wajen gina katafaren gida a cikin unguwar Maitama da ke Abuja, wanda akalla zai kai naira bilyan 1 da miliyan 200.

A matsayin Dikko na babban hafsan hafsoshin sojojin sama a lokacin sa, shi ya rika bugun kirjin bada umarnin a cire ko a debi kudade ga babban jami’in kula da kudaden bangaren ayyukan sojin sama.