Home Labaru Bangaren Tsaro: Shugaba Buhari Ya Ce A Shirye Yake Ya Sake Yin...

Bangaren Tsaro: Shugaba Buhari Ya Ce A Shirye Yake Ya Sake Yin Garambawul

74
0
Kudurin Man Fetur

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin yin iya bakin kokarin sa domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi kasa  inda yake cewa ba zai yarda ya bar gwamnati a matsayin wanda ya gaza ba.

Shugaban kasa yace a shirye yake ya gudanar da karin sauye sauye a bangaren tsaron kasar domin ganin an cimma biyan bukata wajen kare lafiya da dukiyoyin jama’a idan bukatar haka ta taso.

Mai ba shugaban shawara akan harkokin tsaro Janar Babagana Monguno ya bayyana wannan matsayin bayan taron majalisar tsaro da aka yi inda shugabannin suka tattauna halin da ake ciki da kuma irin nasarorin da ake samu sakamakon nada sabbin hafsoshin soji da ‘yan sandan da akayi.

Monguno yace mika kan da daruruwan mayakan boko haram keyi hannun sojojin Najeriya na daya daga cikin nasarorin da gwamnati ke samu wajen yaki da ‘yan ta’adda a arewa maso gabash, yayin da shugaban kasa ya yaba da yadda ake samun hadin kai sosai tsakanin hukumomin tsaron da ake da su sabanin yadda abin yake a shekarun baya.