An samu hauhawar farashin kayayyaki a Amurka, hauhawar da ba a taɓa samu ba kusan shekara 40.
Farashin ya tashi da kashi 6.8 cikin 100 a watan Nuwamba idan aka kwatanta da ƙididdigar da aka bayar a Nuwambar bara.
Farashin fetur da abinci da hayar gida duk sun bayar da gudunmawa wajen hauhawar farashin.
A jiya Alhamis, Shugaban ƙasar Joe Biden ya ce duk da ƙididdigar da ke cewa a yanzu farashi ya hau, amma ba da daɗewa ba farashin zai sauka.
You must log in to post a comment.