Home Home Bai Kamata A Ba Emefiele Hutun Zuwa Karo Karatu Ba –Matawalle

Bai Kamata A Ba Emefiele Hutun Zuwa Karo Karatu Ba –Matawalle

88
0

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle Maradun, ya kalubalanci matakin ba Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele dama ya tafi hutun karo karatu a kasashen waje.

Matawalle, ya ce akwai bukatar Emefiele ya tsaya ya yi bayani game da shirin samar da sabbin kudade da ya kirkiro, wanda ya jefa al’umar Nijeriya cikin mummunan yanayi.

Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata rahotanni sun yi nuni da cewa Shugaba Buhari ya sahale wa Emefiele tafiya hutun karo karatu a kasar waje.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamna Matawalle, ya nemi Buhari ya soke hutun, domin Emefiele ya na da tarin batutuwan da ya kamata ya yi bayani a kai ga sabuwar gwamnatin da ke shirin karbar mulki.

Ya ce ya na bukatar kada Shugaba Buhari ya amince da hutun zuwa karo karatu ga duk wani ma’aikacin da ke da muhimmiyar rawar da zai taka wajen ganin sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara aiki.

Leave a Reply