Home Home An Sanya Dokar Hana Fita Wani Yanki Na Jihar Filato

An Sanya Dokar Hana Fita Wani Yanki Na Jihar Filato

281
0

Hukumomi a jihar Filato, sun sanar da sanya dokar hana zirga-zirga a yankin Bwai da ke ƙaramar hukumar Mangu.

Wata sanarwa da shugaban ƙaramar hukumar Mangu Minista Daput ya fitar, ta ce an amince da sanya dokar ne domin dawo da zaman lafiya bayan wani hari da aka kai, wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayukan kimanin mutane 20.

Bayanai sun nuna cewa, wasu mahara ne su ka afka wa ƙauyukan suka cinna wa gidajen mutane wuta, sannan su ka harbin wadanda ke ƙoƙarin tserewa.

Wata majiya ta ce, ana ci-gaba da bincike domin gano ko akwai sauran waɗanda su ka mutu ko su ka raunata sakamakon harin.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato DSP Alfred Alabo, ya ce sun tura ƙarin jami’an su domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da bincike.

Leave a Reply