Home Labaru Badakalar Makamai: Jam’iyyar APC Ta Bukaci A Yi Gaugawar Kama Ibikunle Amosun

Badakalar Makamai: Jam’iyyar APC Ta Bukaci A Yi Gaugawar Kama Ibikunle Amosun

339
0

Jam’iyyar APC ta yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro su gaggauta tasa keyar tsohon gwamna Ibikunle Amosun saboda safarar dubban makamai da ya yi zuwa jihar Ogun.

Kakakin jam’iyyar APC reshen jihar Ogun Tunde Oladunjoye ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya ce muddin ba dauki mataki a kan Amosun ba an ci mutuncin doka, domin abin da ya yi ba karamin tashin hankali ne ba.

Oladunjoye ya kara da cewa, jihar Ogun sun ga bala’o’i da masifu a karkashin mulkin Amosun, domin an rika yawo da makamai ana kashe masu mutane ba bisa ka’ida ba, musamman a lokacin zabe. Ya ce ya kama a nemi bahasin yadda ya shigo da wadannan dubban bindigogi da miliyoyin harsasai zuwa cikin jihar Ogun, domin gwamna ba ya da ikon shigo da irin wadannan makamai gaba-gadi ba tare da lasisi ba.