Home Labaru Kiwon Lafiya Yaki Da Shaye-Shaye: Mutane Miliyan 35 Ke Fama Da Matsalar Shan Kwayoyi...

Yaki Da Shaye-Shaye: Mutane Miliyan 35 Ke Fama Da Matsalar Shan Kwayoyi – MDD

847
0

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce, kimanin mutane miliyan 35 ne aka kiyasta cewa su na fama da matsalar miyagun kwayoyi a duniya, fiye da yadda aka yi tsammani tun farko.

An dai fitar da rahoton ne, yayin da aka bayyana Laraba 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da fatauci da miyagun kwayoyi ta duniya, kuma Nijeriya ta kasance daya daga cikin kasashen da ke fama da wannan matsala.

Idan dai za a iya tunawa, a baya Majalisar dokoki ta tarayya  ta ce, kimanin kwalaben maganin tari mai sinadarin kodin miliyan uku ake shanyewa a jihohin Kano da Jigawa a kowace rana. Haka kuma, wani bincike da BBC ta yi a shekarar da ta gabata, ya kai ga rufe wasu manyan kamfanonin sarrafa magunguna tare da haramta saida maganin tarin mai sinadaran Kodin da Tramadol a Nijeriya. 

Leave a Reply