Home Home Babu Mahalukin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi

Babu Mahalukin Da Zai Hana Rantsar Da Tinubu – Sarkin Musulmi

102
0

Mai Alfamar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce babu mahalukin da zai dakatar da rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Basaraken ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen wani taro da Bankin Duniya ya shirya a Abuja, inda ya ce maimakon ƙoƙarin dagula wa lamarin lissafi, kamata ya yi ’yan Nijeriya su himmantu da yi wa gwamatin Tinubu addu’a da fatan nasara.

Ya ce dole a samu canji, saboda nan da ‘yan kwanaki ko makonni za a samu sabuwar gwamnati, kuma dole hakan za ta kasance, don haka babu abin yi illa addu’a, don kuwa mun yi imani da Ubangiji, mun yarda cewa Shi ke bayarwa, kuma Shi ke karɓewa. A karshe Sarkin Musulmi ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su haɗa kai, tare da yin aiki tare domin ci-gaban ƙasa

Leave a Reply