Home Labaru Zagon Kasa A Zaben 2023: Jam’Iyyar APC Ta Kafa Kwamitin Bincike A...

Zagon Kasa A Zaben 2023: Jam’Iyyar APC Ta Kafa Kwamitin Bincike A Zamfara

36
0

Jam’iyyar APC a jihar Zamfara, ta kafa kwamitin binciken
zagon kasa da wasu ‘yan jam’iyyar su ka yi, na nuna adawa
ga ‘yan takarar jam’iyyar a zaben da ya gabata.

Kwamitin dai, an kafa shi ne a karkashin jagorancin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jiha Malam Yusuf Idris Gusau.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara Tukur Umar Danfulani ne ya jagoranci kaddamar da kwamitin a
sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau.

Tukur Umar Danfulani, ya bukaci ‘yan kwamitin su yi nazari a kan duk wasu zarge-zargen da ake yi wa kowa, ko da kuwa ya na daga cikin jigajigan jam’iyyar, domin tabbatar da cewa ya na da hannu wajen yi wa jam’iyyar zagon kasa, tare da samar da matakan da za a dauka a kan sa.

Ya ce tuni sakatariyar jam’iyyar ta jiha ke rike da kwafin koke-koke a kan wasu ‘yan Jamiyyar, ya na mai cewa kwamitin ya kamata ya gudanar da aikin sa ba tare da tsoro ko son rai ba.

Leave a Reply